Isa ga babban shafi
Nijar

Nijar na fama da mummunar ambaliyar ruwa

Ambaliyar ruwa na ci gaba da shafar sassa da daman a jamhuriyar Nijar, inda a garin Mayayi da ke jihar Maradi, ruwan sama da ya rika sauka a ‘yan kwanakin nan ya haddasa barna ga gidaje, konaki tare da asarar rayuwar akalla mutum daya.

Ambaliya a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo
Ambaliya a birnin Kinshasa na Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo JUNIOR D.KANNAH / AFP
Talla

Wasu yankunan da ambaliyar ta tsananta sun hada Dogarawa da ke jihar Tawa, inda a cikin sa’o’I 24 aka samu kusan milimita 170, lamarin da ya haddasa rushewar gidaje masu tarin yawa.

A kwanakin da suka gabata, hukumar kula da ayyukan jinkai ta Majalisar Dinkin Duniya OCHA, ta yi has ashen cewa za su samu mummunar ambaliya a kasar ta Nijar.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.