Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya yi tir da kisan Kararuza

Shugaban Burundi, Pierre Nkurunziza ya yi Alla-wadai da kisan da aka yi wa wani babban jami’in sojin kasar ta hanyar harbe shi da bindiga tare da matasrsa da dogarinsa a jiya Litinin.

Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban kasar Burundi Pierre Nkurunziza REUTERS/Evrard Ngendakumana
Talla

An dai kashe Birgediya Janar Athanase Kararuza ne a lokacin da ya ke hanyarsa ta zuwa wata makarantar boko a mota domin ajiye dansa a kusa da babban birnin Bujumbura, yayin da wasu suka yi wa motar ruwan harsashai.

Marigayin ya rike mukamin mashawarci kan harkokin soji a ofishin mataimakin shugaban kasar, sannan kuma a can baya, ya rike mukamin mataimakin kwamandan rundunar wanzar da zaman lafiya a jamhuriyar Afrika ta tsakiya.

A cikin wata sanarwar da ya fitar, shugaba Nkurunziza ya ce, Mr. Kararuza ya yi yaki tukuru da jami'an da suka yi yunkurin juyin mulkin kasar a bara, kuma ya bada gudun mawa wajen tabbatar da tsaro da zaman lafiya a lokacin zaben Burundi.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.