Isa ga babban shafi
Ghana

An gargadi Ghana akan barazanar hare haren Ta’addanci

Hukumar shige da fice a Ghana ta gargadi gwamnatin kasar da Togo akan barazanar hare haren ta’addanci da za a iya kai wa kasasashen biyu a bana irin wadanda aka taba kai wa a kasashen Burkina Faso da Cote d’Ivoire.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama
Shugaban Ghana John Dramani Mahama Screen capture
Talla

Hukumar shige da ficen ta bukaci daukar matakai a kan iyakokin kasar a cikin wata takarda da ta aikawa gwamnatin Ghana a ranar 9 ga watan Afrilu.

Hukumar tace mayakan Mali barazana ce ga tsaron Ghana, kuma suna da tabbaci daga jami’an tsaron Cote d’Ivoire da suka tatsi bayanai daga mutumin da ake zargi ya jagoranci harin da aka kai wa kasar a ranar 13 ga watan Maris da ya kashe mutane 18.

Sakon gargadin ga gwamnatin Ghana ya bukaci a tsaurara matakan tsaro a kan iyakokin kasar da Burkina Faso.

Tuni dai mayakan Al Qaeda reshen Afrika suka dauki alhakin hare haren da aka kai a otel otel a kasashen Mali a watan Nuwamba da Burkina Faso a watan Janairu da kuma wanda aka kai a Cote d’Ivoire.

Sama da mutane 65 suka mutu a hare haren, kuma yawancinsu yan kasashen waje ne.

Amma Ghana na cikin kasashen Afrika da ke cikin kwanciyar hankali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.