Isa ga babban shafi
Ghana

Ghana za ta Rika Bada Takardun Shiga Ba tare da Jibin Goshi ba daga Watan August

Shugaban Ghana John Dramani Mahama ya sanar da cewa daga watan bakwai mai zuwa kasar za ta rika baiwa masu son shiga kasar daga kasashen Africa 54 takardan izinin shiga wato Visa da zaran sun tsoma kafa cikin kasar.

Shugaban Ghana John Dramani Mahama
Shugaban Ghana John Dramani Mahama Screen capture
Talla

Shugaban wanda yake jawabi a bukin samun ‘yancin kan kasar karo na 59 ya ce an dauki wannan mataki ne domin saukaka wahalar samun takardun izinin shiga.

Bada takardan izinin zama akasar zai samu cikin sauki, da bada damar zama na tsawon wata daya cur, don ganin irin abubuwan da Allah ya horewa Ghana.

Karkashin tsohon tsarin  kasar Ghana kan bar wadanda ke kasashe 15 ne kawai na kungiyar kasashen yammacin Africa, ECOWAS/ CEDEAO damar su shiga kasar ba tare da takardun izinin ba.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.