Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Za a ci gaba da zabe a wasu yankunan Jamhuriyar Nijar

Wallafawa ranar:

Rahotanni daga Iferouane dake Jamhuriyar Nijar sun ce an dage gudanar da zaben shugaban kasar da akayi jiya saboda rashin isar kayan aiki, yayin da aka samu tsaiko a wasu Yankunan kasar.Yayinda Kungiyar Tarayyar Afrika ta yaba da halayen ‘Yan Nijar kan yadda suka gudanar da babban zaben kasar cikin kwanciyar hankali ba tare da samun wata hatsaniya ba.

Wasu daga cikin masu zabe
Wasu daga cikin masu zabe
Talla

An gudanar da zaben ne cikin tsauraran matakan tsaro inda aka tanadi ababan hawa masu yawa da sukayi sintiri domin ganin anyi komi cikin kwanciyar hankali.
‘Yan takara 15 ne suka fafata a zaben, ciki har da shugaban kasa Mahammadou Isoufou da ke neman wa’adi shugabanci na biyu.

Za gudanar da wadannan zabubuka ne a jihohin da suka hada da Tahoua,Zinder da Agadez.

Kuma an gudanar da zaben ne yayin da guda daga cikin ‘yan takarar kuma tsohon shugaban majalisar kasar Hama Amadou ke tsare a gidan kaso.
Bashir Ibrahim Idris ya tattauna da Lydia Ado wakiliyar mu a Jamhuriyar ta Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.