Isa ga babban shafi
Najeriya

Buhari ya nada Mustapha Magu shugaban EFCC

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nada Ibrahim Mustapha Magu a matsayin shugaban hukumar EFCC da ke yaki da masu yi wa tattalin arziki zagon kasa, wanda ya maye gurbin Ibrahim Lamorde da aikin sa zai kare a watan Fabarairu mai zuwa.

Tambarin hukumar EFCC da ke yaki da tu'amulli da kudaden jama'a a Najeriya
Tambarin hukumar EFCC da ke yaki da tu'amulli da kudaden jama'a a Najeriya RFI / Pierre Moussart
Talla

Sanarwar da Femi Adeshina mai bai wa Buhari shawara kan harkokin yada labarai ya fitar, ta nuna cewar Magu na cikin ‘yan kwamitin da ke ba shugaban shawara kan yadda za a inganta yaki da cin hanci da rashawa a fadin Najeriya

Sanarwar tace Magu ya taba aiki a hukumar EFCC a karkashin Nuhu Ribadu kuma ya jagoranci binciken da suka hada da rugujewar Societe General Bank da kuma tsohon Gwamnan Delta James Ibori.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sha alwashin magance matsalar Yaki da cin hanci da Rashawa a Najeriya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.