Isa ga babban shafi
Najeriya

Shugaban MTN ya yi murabus kan tarar da Najeriya ta ci kamfanin

Shugaban Kamfanin sadarwa na MTN Sifiso Dabengwa na kasar Afrika ta kudu ya bayyana yin murabus a yau Litinin kan tarar kudi dala biliyan 5.2 da Najeriya ta ci kamfanin.

MTN office in Ikoyi Lagos Nigeria
MTN office in Ikoyi Lagos Nigeria 8brand.co
Talla

A cikin wata sanarwa, kamfanin ya sanar da nada Phuthuma Nhleko a matsayin shugaba na wuccin gadi na tsawon watanni shida kafin a nada wanda zai gaji Dabengwa.

Hukumomin Najeriya sun ci tarar kamfanin na MTN ne saboda rashin dakatar da layukan da ba su da rajista aiki a kasar.

Yanzu haka kuma hukumar hada hadar hannayen jari a Johannesburg ta kaddamar da bincike kai bayan darajar hannayen jarin kamfanin ya fadi

Bayanai sun nuna cewar hukumar sadarwar Najeriya taci tarar kanfanin naira 200,000 kan kowanne layi da ake amfani da shi wanda ba shi da rajista.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.