Angola
An kama masu yi wa 'yan adawa addu'a a Angola
'Yan Sanda a kasar Angola sun kama mutane 20 da suka kwashe dare suna addu’a ga 'yan adawar da aka tsare cikin su har da wani fitaccen mawaki Luaty Beirao, wanda aka tsare tun watan Yuni.
Wallafawa ranar:
Talla
Rahotanni sun ce akalla mutane 100 suka taru a wata Mujami’a da ke Luanda domin addu’ar ganin an saki mutanen 15 da aka tsare, saboda zargin da ake musu na yunkurin kifar da gwamnati.
Su dai mutanen na bukatar ganin shugaban kasar Jose Eduardo Dos Santos wanda ke karagar mulki tun shekarar 1979 ya sauka daga mukaminsa ne.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu