Isa ga babban shafi
Mali

ICC za ta fara shari'ar Al-Faqi na Mali

 A yau laraba ne ake saran kotun hukunta manyan laifufuka ta duniya dake Haque za ta fara sauraron tuhumar da ake yiwa Ahmad Al-Faqi Al-Mahidi, daya daga cikin shugabannin 'Yan Tawayen Mali da ake zargi da lalata wuraren tarihin a Timbuktu. 

Ana zargin Al-Faqi da lalata kaburburan Shaihannan Malaman Kasar Mali.
Ana zargin Al-Faqi da lalata kaburburan Shaihannan Malaman Kasar Mali.
Talla

Za a  tuhumi Al- Faqi, shugaban wanda ake kira Abu Tourab  da laifuffukan yaki kuma a karon farko kenan da zai bayyana a gaban Kotun tun bayan da sojojin Jamhuriyyar Nijar suka mika shi ga jami’an kotun a ranar Asabar

A watan Yunin bara ne Yan Tawayen  Ansaruddine da Al-Faqi ke jagoranta suka lalata wuraren tarihi da suka hada da makabartar Shaihunan malamai na karnin 15 da 16.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.