Isa ga babban shafi
Libya

MDD ta bukaci masu adawa da juna a Libya su warware sabaninsu

Manzon musamman na MDD a kasar Libya Bernardino Leon, ya ce majalisar ba za ta sake shirya zama domin tattaunawa a tsakanin bangarori masu hamayya da juna a kasar ba, inda ya bukaci tawagogin da suka halarci tattaunawar da aka yi a birnin Shihirat na kasar Maroko da su rungumi zaman lafiya a cikin gaggawa.

Bernardino Leon, manzon musamman na MDD a Libya
Bernardino Leon, manzon musamman na MDD a Libya REUTERS/Stringer
Talla

A kasar Libya dai akwai majalisun dokoki biyu, to sai dai daya daga cikinsu ce kawai ta samu amincewar kasashen duniya, to sai dai wannan ya kasance karo na farko da wakilan majalisun biyu suka zauna kan teburi domin sulhu a tsakaninsu.

A yanzu dai Majalisar Dinkin Duniya ta danka alhakin dawo da zaman lafiyar ne a hannun bangarorin da ke hamayya da juna a kasar ta Libya, wadda ke fama da rikici tun bayan faduwar gwamnatin Mu’ammar Kaddafi a shekara ta 2011.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.