Isa ga babban shafi
Najeriya

‘Yan Boko Haram sun fara mika wuya ga Sojin Najeriya

Wasu daga cikin mayakan Boko Haram sun mika wuya ga dakarun Najeriya wadanda ke ci gaba da fatattakarsu a yankin arewa maso gabashi da mayakan suka addaba.

Dakarun Najeriya na smaun galaba akan Boko Haram
Dakarun Najeriya na smaun galaba akan Boko Haram dailypost.ng
Talla

Daraktan yada labaran rundunar Kanal Sani Usman Kukasheka ya ce mayakan da dama sun mika wuya bayan sun ga uwar-bari.

A cewarsa mayakan sun fara mika wuya ne saboda sabon salon da rundunar sojin Najeriya ta dauka na yaki da mayakan musamman ruwan wuta da ake ma su ta sama da kasa.

Sannan ya ce an dakile duk wata hanya da mayakan ke samun taimako.

Kanal Kukasheka ya kara da cewa karbe ikon Gamboru Ngala ya taimaka wajen tarwatsa Boko Haram.

A  lokacin da ya ke ziyara a Ghana a makon jiya, Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dakarun Najeriya na smaun galaba akan Boko Haram.

Kanal Kukasheka ya shaidawa RFI Hausa cewa yanzu haka suna tatsar bayanai daga shugabannin mayakan Boko Haram da suka cafke a lokacin da suka karbe Gamboru Ngala.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.