Isa ga babban shafi
Libya

Mayakan ISIL sun File kawuna mutane 12 a Libya

Mayakan ISIL sun file kawuna wasu mutane 12 tare da rataya su a yankin Sirte da ke kasar Libya, kamar dai yadda kamfanin dilancin labaran LANA suka rawaito.Rahotanin sun ce wadanda aka fille kawunan na su kanana ‘yan bindiga ne da ke gwabza rikicin kare yankinsu daga ISIL.

Talla

Rikcin iko da yankin Sirte garin tsohon shugaban kasar marigayi Moamer Kadhafi ya fara ne tun a cikin ranar talata da ta gabata, rikicin da wani babban jami’an diflomasiya kasar ya gargadi aikata kisan gila a yankin.

Majiyoyin sun rawaito cewa Mayakan sun kuma kashe wasu mazauna Sirte 22 wanda ke kyamar ayyukanta tare da jikata wasu da dama dake asibiti.

Kamfanin dilanci Labaran Faransa ta jiyo Hukumomin yanke na cewa rikici na sake kamari a yau assabar, bayan kona wani babban asibiti garin da Mayakan Jihadi suka yi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.