Isa ga babban shafi
Najeriya

An kusan fara shari’ar barayin gwamnatin Najeriya

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayyana cewar nan da ‘yan makwanni masu zuwa za a fara gudanar da shari’ar barayin da suka yi rub da ciki da kudaden talakawa.

Shugaban Najeriya  Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osibanjo tare da tawagar Kwamitin Zaman lafiya karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da Mataimakinsa Yemi Osibanjo tare da tawagar Kwamitin Zaman lafiya karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Abdulsalami Abubakar ekpoesitons
Talla

Shugaban ya bayyana haka lokacin da ya karbi tawagar kwamitin zaman lafiya a karkashin jagorancin tsohon shugaban kasa Janar Abdussalami Abubakar a fadarsa a Abuja.

Shugaban ya ce a shirye ya ke ya yi duk iya bakin kokarinsa don kawo karshen cin hanci da rashawa a Najeriya da rashin ayyukan yi da kuma matsalar tsaro a kasar.

Buhari ya ce babu yadda za a ci gaba idan ana samun barayin dukiyar Jama’a a cikin al’umma. Kuma Shugaban ya tabbatar da cewa sun tattara bayanai akan Barayin.

‘Yan kwamitin na zaman lafiya sun bukaci Shugaban ya bi doka da oda wajen hukunta barayin gwamnati.

Bishop Mathew Kukah, daya daga cikin ‘Yan kwamitin na zaman lafiya ya yi watsi da zargin da wasu ke yi kan sun je wajen Buhari don neman wa wasu jami’an tsohuwar gwamnati alfarma kan binciken rashawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.