Isa ga babban shafi
Faransa-Kamaru

Bayanan Hollande lokacin ganawarsa da Biya

Shugaban Faransa Francois Hollande wanda ke ganawa da shugaban Kamaru Paul Biya a birnin Yaounde a ranar juma’a, ya jaddada goyon bayansa ga kokarin da kasar ta Kamaru ke yi wajen yaki da kungiyar Boko Haram wadda ta samo asalin a Najeriya.

François Hollande da Paul Biya lokacin ganawarsu ranar 3 ga watan yulin 2015 a birnin Yaoundé.
François Hollande da Paul Biya lokacin ganawarsu ranar 3 ga watan yulin 2015 a birnin Yaoundé. AFP PHOTO / ALAIN JOCARD
Talla

Ko baya ga batun tsaro, haka zalika shugaban na Faransa wanda ke gabatar da taron manema labaran hadin-gwiwa da takransa na Kamaru, ya tabo batun gina dimokuradiyya, kare hakkin bil’adama da kuma samun ‘yancin fadin albarkacin baki a kasar.

Shugaban na Kamaru dai ya share shekaru 33 akan karagar mulki, yayin da abokannin hamayyarsa na siyasa da kuma masu fafutukar kare hakkin dan adam ke kallon sa a matsayin wanda ke kawo cikas ga yunkurin samar da sauyi a kasar.

Hari ila yau shugaba Hollande ya amince Faransa ta yi amfani da hanyoyi na azabtarwa wajen murkushe ‘yan aware magoya bayan jam’iyyar UPC da suka yi yunkurin ballewa daga Kamaru, inda sojojin na Faransa da kuma kananan sojojin Kamaru suka kashe dubban mutane a lokacin.

Wannan ne karo na farko a cikin shekaru 16 da wani shugaban Faransa ke kai ziyara a Kamaru.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.