Isa ga babban shafi
Masar-Spain

Amnesty ta yi fatali da ziyara al-sisi zuwa Spain

Kungiyoyin kare hakkin bil’adama sunyi fatali da ziyara da shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-sisi ya kai kasar Spain, tare da bayyana gwamnatinsa a matsayin ta ci da karfi. Wannan dai na zuwa ne, bayan Sarkin kasar Spain Felipe na 11, ya gayyace al-sisi domin tattauna batun cigaba kasashen biyu, da kuma ingata huldar diflomasiya.

shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi
shugaban kasar Masar, Abdel Fattah al-Sisi REUTERS/Amr Abdallah Dalsh
Talla

Wannan dai shine karon farko da wani shugaban kasar masar ya kai ziyara Spian, tun bayan shekarar 2006, adai-dai lokacin da rikicim gabas ta tsakiya ke daukan hankula kasashen yammci, musamma abubuwa da ke faruwa a kasar libya, da sudan, da syria da kuma Yemen

Ziyara al-sisi na kwana guda, na samun gagarumin suka daga kungiyar Amnesty International dama sauran kungiyoyin kare hakkin bil’adama, inda suka bukaci firiya Minista Spian Mariano Rojoy ya ja hankali al-sisi akan muhimmaci hakin bil’adama yayyin zantawar su

Sarkin Spain Felix na 11 na gani cewar, a wannan lokaci da abubuwa ke cigaba da dagulewa a gabas ta tsakiya, masar nada gagarumin rawar da zata iya takawa wajen daidaita al’ummura

kasashen biyu dai sun sanya hannu akan yarjejeniya da dama, kama da batutuwa yawon bude ido, al’adu da sauransu

Rahotanin dai na cewa, ana zargin al-sisi da kawar da ‘yan adawa a kasar Masar domin cimma bukatun sa na aiwatar da gwamnatin ci da karfi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.