Isa ga babban shafi
Kenya

An rufe hanyoyin aika kudade a Kenya saboda ta'addanci

Hukumomin kasar Kenya sun sanar da rufe hanyoyin aika  kudade guda goma sha uku zuwa kasar Somalia, a wani mataki na hana kungiyar El shabab samun kudaden da suke anfani dasu wajen kai munanan hare hare

'Yan Kungiyar Al-shebab
'Yan Kungiyar Al-shebab REUTERS/Feisal Omar
Talla

Daukar wannan matakin da hukumomin kasar Kenya suka yi, ya biyo bayan kazamin harin da kungiyar Al-shebab ta kai da ya hallaka mutane 147 a makon da ya gabata.

Tuni dai yan Somalia mazauna kasar suka soma bayyana rashin amincewarsu da matakin ganin yawancinsu sun dogara da wannan hanya domin aika kudi zuwa ga 'yan uwansu da ke Somalia, a yayin da hukumomin Kenya ke zargin yan ta’adda da amfani da irin wadannan hanyoyi wajen samun kudin dake basu damar sayan makaman da suke kai hare hare akan jama’a.

Ana  cigaba da cece kuce tsakanin al’ummar kasar Somaliaa dake da yawan gaske acikin kasar da gwamnatin Kenya.

Duk da haka gwamnatin Kenya ta kare kanta da daukar wannan matakin da tace zai taimaka a sabbin matakan tsaron da ta ke shiryawa na kare al’ummar kasar .

wannan na zuwa ne sakamkon mummunar harin da 'yan kungiyar al-Shebaab suka dauki alhakin kaiwa a jami'ar Garissa da ke Kenya, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar akalla mutane 147.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.