Kenya ta ayyana zaman makoki akan harin Jami’a
Gwamnatin kasar Kenya ta ayyana kwanakin makoki akan harin da Mayakan kungiyar al-Shebab suka kai wa Jami’ar Garissa a makon jiya abinda ya yi sanadin mutuwar Dalibai da dama
Wallafawa ranar:
Akalla dai Dalibai 148 ne suka mutu a harin mamayar da Kungiyar ta ka iwa Jami’ar har na tsawo Awa 15.
Shugaban kasra Kenya Uhuru kenyatta kuma ya bayyana cewar yanzu haka an yiwa maharan Kofar-Rago a cikin kasar inda yanzu haka ake tsare da wasu mutum 5 da ake zargi da Hannu a ciki.
Hudu daga cikin wadanda ake zargin dai ‘yan kasar Kenya ne, a yayin da na 5 daga cikinsu kuma dan kasra Tanzaniya ne, a yayin da babban wanda ake zargin ya hau kafafuwansa.
Shugaban kasar kenya Uhuru kenyatta ya bukaci al’ummar musulmin Kenya da yace suna da halayen kirki da su taimaka a gano sauran maharan da suka gudanar da wannan danyen aiki.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu