Isa ga babban shafi
Najeriya

'Yan Nigeria na ci gaba da bayyana ra'ayoyin su kan amfani da Card Reader

Jiya aka gudanar da zaben shugaban kasa a Nigeria, inda a karon farko aka yi amfani da na’urar tantance masu kada kuri’a ta Card Reader. An yi ta cecekuce kan amfani da na’urar, da hukumar zaben kasar tace zata taimaka wajen rage magudin zabe daya zama ruwan dare a kasar.Tun da sanyin safiyar jiya Asabar ‘yan Nigeria suka fara dandazo a runfunan zaben dake fadin kasar, da nufin tantance su su kada kuri’a cikin lokaci, sai dai kuma an sami matsala a wasu wuraren da dama, inda aka yi ta fama da na’urar kafin ta tantance jama’a, a wasu wuraren kuma an dage zaben har zuwa yau Lahadi.Lokacin da yake hira da gidan Radiyon Faransa, Gwamnan Jihar Neja, mu’azu babangida Aliyu yace shi bai ga alfanun na’urar ba.Rahonni na cewa sai da aka yi fama kafin tantance shugaba Goodluck jonathan, da Gwamnan jihar Adamawa James Nglari.Sai dai duk da wannan ‘yan kasar da dama suna ganin amfani da na’urar zata taimaka wajen rage magudin zabe.Suma kwararraru na ganin kwalliya ta biya kudin sabulu a harkar, kamar yadda Dr Abdulhakeem Garba na Jami’ar Dundee a kasar Scotland ke cewa.Yanzu abin jira a gani shine yadda hukumar zabe ta INEC zata shawo kan matsalolin da aka samu wajen amfani da na’urar.  

Na'urar tantance katin zabe ta Card Reader a Najeriya
Na'urar tantance katin zabe ta Card Reader a Najeriya REUTERS/Goran Tomasevic
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.