Kungiyar Ecowas ta bukaci a dage zabe a Togo
Kungiyar Kasashen Afrika ta Yamma wato ECOWAS ta bukaci jinkirta gudanar da zaben shugaban kasar Togo saboda abinda ta kira korafe korafen yan adawa wajen rubuta sabon rajistar masu kada kuri’u.Ana cigaba da samu tashe-tashen hankula a wasu biranen kasar, yayi da yan adawa ke cigaba da yi kira zuwa Shugaban kasar Faure Gnassigbe da ya kaucewa sake neman kujerar shugabancin kasar ta Togo.
Wallafawa ranar:
Shugaban Kasar Ghana John Dramani Mahama dake shugabancin kungiyar ya bayyana haka lokacin da ya ziyarci kasar Togo.
Kungiyoyin fararen hula a kasar dama wasu daga cikin yan siyasa na fatar gani hukumar zabe ta yi naam da wanan bukata daga kungiyar kasashen Afrika ta yama Ecowas.
Hakan kuma wata hanyar ceto kasar ta Togo daga fadawa cikin wani sabon rikicin siyasa inji Shugaban kasar Ghana kuma Shugaban kungiyar Ecowas.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu