Isa ga babban shafi
Nijar-Najeriya

Sojojin Chadi da Nijar sun kwace Damasak daga Boko Haram

Rahotanni daga Najeriya na cewa, sojojin Jamhuriyar Nijar da na Chadi, sun samu nasarar kwace garin Damasak na tarayyar Najeriya daga hannun ‘yan kungiyar Boko Haram, yayain da wasu bayanai ke cewa an kashe mayakan kungiyar ta Boko Haram su akalla 200 daga jiya zuwa yau.

Taswirar jamhuriyar Nijar dauke da yankuna cikinsu har da Diffa
Taswirar jamhuriyar Nijar dauke da yankuna cikinsu har da Diffa (Carte : RFI)
Talla

Mai magana da yawun rundunar sojan Jamhuriyar Nijar Kanar Mishel Ledri, ya tabbatar wa sashen Hausa na rediyo Faransa cewa yanzu haka dakarun kasashen biyu na ci gaba gwabza fada da mayakan na Boko Haram a wani wuri da ke cikin tarayyar Najeriya.

Wasu majiyoyin kuwa sun bayyana cewa an kashe sojojin Chadi 10 tare da raunata wasu 20, yayin da wasu rahotanni ke cewa akwa wasu sojoji akalla 33 da aka kwantar a asibitin birnin Diffa da ke cikin jamhuriyar Nijar.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.