Isa ga babban shafi
Najeriya-Faransa

Faransa na kokarin sasanta Najeriya da makwabtanta

Kasar Faransa tace za ta taimaka wajen jagorancin wani shirin kasashen Afirka ta Yamma don yaki da kungiyar Boko Haram saboda yadda ake samun rashin jituwa a tsakanin Najeriya da kasashen ke makawabtaka da ita.

Shugaban Faransa Francois Hollande  tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Paris
Shugaban Faransa Francois Hollande tare da Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan a Paris REUTERS/Gonzalo Fuentes
Talla

Ministan tsaron kasar Jean-Yves Le Drian da ke magana a Senegal yace matakin ya biyo rashin yarda da ya fito karara tsakanin kasashen yammacin Afrika da ke makwabtaka da Najeriya

Faransa tace zata jagoranci shirin kafa rundunar mai dauke da sojoji 2,800 tsakanin kasashen hudu domin yakar Mayakan Boko Haram.

A wata ganawa da suka yi a birnin Paris, Najeriya da Nijar da chadi da Kamaru sun amince su yi musayar bayanan sirri a tsakaninsu da suka shafi kula da kan iyakokinsu da daukar matakan da suka dace, amma alamu na nuna kasashen hudu sun ki amincewa da juna.

Faransa ta yi watsi da daukar matakin Soji amma za ta taka muhimmiyar rawa wajen hada kan Najeriya da kasashen da makwabtaka da ita.

Masu sharhi sun ce makwabtan Najeriya suna zargin akwai hannun Sojojin kasar a rikicin Boko Haram don haka suke dari-dari.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.