Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta karbe Damasak a Borno

Mayakan Boko Haram sun bude wuta a kasuwar garin Damasak a karamar hukumar Mobbar a jihar Borno, rahotanni sun ce mayakan kuma sun kafa tutarsu bayan sun yi musayar wuta da Jami’an tsaro.

Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau
Mayakan Boko Haram, tare da shugabansu Abubakar Shekau AFP PHOTO / BOKO HARAM
Talla

Wani mutumin garin ya shaidawa RFI Hausa cewa Mayakan sun yi musayar wuta da Jami'an tsaro bayan sun abkawa kasuwar garin da ke ci a ranar Litinin.

Mutumin garin wanda ya nemi a sakaye sunansa ya ce mutane da dama sun jikkata yayin da wasu ke kwance a mace.

Zuwa wannan lokaci an kasa kididdige yawan mutanen da suka yi hasarar rayukansu sakamakon harin da Mayaka na kungiyar Boko Haram suka kai.

Garin Damasak dai na kan iyaka ne da Jamhuriyyar Nijar

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.