Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram: Iyayen Matan Chibok sun shiga damuwa

Mutanen garin Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace ‘yayansu sama da 200 tsawon watanni shida babu duriyarsu, sun ce sun kadu matuka da jin ikirarin Abubakar Shakau akan ya daurawa ‘Yan Matan aure a cikin wani sabon sakon bidiyonsa.

Mutanen garin Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace 'yayansu.
Mutanen garin Chibok da Mayakan Boko Haram suka sace 'yayansu. Reuters/Stringer
Talla

A cikin sakon na bidiyo da aka aikawa Kamfanin dillacin labaran Faransa, Shugaban Mayakan Boko Haram Abubakar Shakau yace dukkanin ‘Yan matan sun karbi addinin Islama yana kuma mai  yin watsi da ikirarin gwamnati na cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta da su.

Hakimin garin Chibok a Jihar Borno Pogo Bitrus yace ikirarin na Boko Haram ya razana su matuka, kodayake yace sun san lamurran Boko Haram babu gaskiya a ciki.

Hakimin yace tuntuni sun san babu kamshin gaskiya ga ikirarin Gwamnati na sasantawa da Boko haram game da ‘ya’yansu, saboda hare haren da Mayakan ke ci gaba da kai wa a yankin arewa maso gabaci.

Akwai ‘yayan ‘yan uwan Hakimin na Chibok guda hudu cikin ‘yan Matan da ke hannun Boko Haram, kuma ya yi kira ga gwamnatin Najeriya ta dauki matakan da duk suka dace domin kubutar da ‘Yan matan.

A ranar 17 ga watan Oktoba ne, rundunar Sojin Najeriya ta yi kirarin cewa ta sasanta da Boko Haram domin kawo karshen zubar da jini a kasar tare da cim ma yarjejeniyar sakin ‘Yan matan Chibok.

Amma duk da wannan ikirarin na gwamnati, Mayakan Boko Haram sun ci gaba da kwace ikon garuruwa tare da dala wani bom a garin Gombe, wanda ya yi sanadin mutuwar mutane takwas tare da jikkata wasu da dama.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.