Isa ga babban shafi
Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya

Dakarun wanzar da zaman lafiya na sauka a jamhuriyar Afruka ta tsakiya

Yanzu haka Dakarun wanzar da zaman lafiya na kasashe daban daban da Majalisar dunkin Duniya ta samar domin kwantar da tarzoma a jamhuriyar Afruka ta tsakiya, na can suna sauka a kasar domin soma aikinsu

nationalturk.com
Talla

Wasu sabbin jami’an sojin da za su yi aikin samar da zaman lafiya daga kasashen Asia da Afrika sun isa Janhuriyar Afrikat a Tsakiya mai fama da tashin hankali.

Rahotanni sun ce akalla sojoji 1,500 da suka fito daga kasashen Bangladesh, da Pakistan, da Indonesia da Morocco ne za su shiga cikin sojojin gamayyar kassahen Nahiyar Afrika 4,800 dan aikin samar da zaman lafiya a kasar.

Yanzu haka dai sojojin Faransa kimanin 2,000 na kasar ta jamhuriyar Afruka ta tsakiya, don taimakawa ga aikin wanzar da zaman lafiyar.

Sai dai a baya an zargi Sojin na Faransa da marawa ‘yan tawayen kungiyar Anti-Balaka baya, da suka yi ta kisan al’ummar Musulmi da basu dauke da makamai a birnin Bangui da ma sauran sassan kasar.

Rikicin Jamhuriyar Afruka ta tsakiya dai ya yi kamari ne bayan bulluwar Kungiyoyin Seleka da Anti-Balaka.

Seleka dai kungiya ce wadda akasarin magoya bayanta Musulmi ne, a yayin da ita kuma Anti-Balaka dukansu Kiristoci ne.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.