Isa ga babban shafi
Masar

Masallatan Masar sun koma karkashin ikon gwamnati

Hukumomi a kasar Masar, sun karbe aikin tafiyar da masallatai masu zaman kansu da ke kasar domin mayar da su a karkashin kulawar hukuma. Irin wannan matakin ne hukumomi a kasar Tunisia ke shirin yin koyi da shi domin kwace aikin tafiyar da dukkanin masallantan kasar.

Jami'ar Al-Azhar a birnin al Kahira
Jami'ar Al-Azhar a birnin al Kahira (Photo : DR)
Talla

Kamfanin dillancin labaran kasar yace hukumomi sun dauki wannan mataki ne domin hana magoya bayan hambararren shugaban kasar Mohammad Morsi ci gaba da yin amfani da masallatan domin yada akidar jam’iyyarsu ta ‘yan uwa musulmi da aka rusa.

Ma’aikatar kula da lamurran addini tace tana bukatar dukkanin masallatan kasar masu zaman kansu zasu dawo karkashinta.

Yawan Masallatan kasar Masar sun kai sama a 130,000, amma gwamnatin Masar tace akwai sama da 10,000 da ba su karkashin kulawarta.

Tuni magoya bayan ‘Yan uwa Musulmi suka fito suna zanga-zangar nuna adawa da matakin.

Tun a watan Janairu ne gwamnatin Masar ta fara tsara maudu’in hudubar masallatan Juma’a a cikin kasar, tare da sallamar Malaman da ke bayar da Salla wadanda ba su yi karatunsu ba a Jami’ar Al-Azhar.

A tsarin dokar Masar yanzu dole sai an tantance Liman kafin ya fara bayar da Sallah a Masallacin Juma’a.

Irin wannan matakin ne hukumomi a kasar Tunisia ke shirin yin koyi da shi domin kwace aikin tafiyar da dukkanin masallantan kasar wadanda gwamnatin tace masu tsatsauran kishin Islama na amfani da su domin yada manufofinsu.

Wani babban jami’I a ma’aikatar harkokin addinai Abdessattar Badr, yace yau makwanni biyu ke nan da suka soma tunanin karbe masallatan, saboda yadda wasu ke amfani da su wajen yada manufofi da kuma yin kira domin kaddamar da jihadi a cikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.