Isa ga babban shafi
Tunisia-Syria

Tunisia: Mayakan Jihadi sun dawo daga Syria

Gwamnatin kasar Tunisia tace mayakan Jihadi kimanin 400 ne suka dawo daga yakin Syria, tare da bayyana fargaba akan dawowarsu na iya hura wutar wani sabon rikici a cikin kasar.

Mayakan al-Nusra, da ke yaki a Syria
Mayakan al-Nusra, da ke yaki a Syria AFP PHOTO/ZAC BAILLIE
Talla

Mayaka da dama ne daga kasashen waje suka shiga Syria domin marawa bangarorin da ke rikici baya, kuma yawancin mayakan sun fito ne daga kasashen Larabawa da kuma wasu daga Rasha da kasashen Turai.

Masana suna ganin banbanci Akida ta Sanni da Shi’a shi ne dalilin da ya sa Mayaka musamman daga kasashen Larabawa suke kwarara zuwa Syria.

An kiyasta cewa kimanin mayakan Jihadi 10,000 ne suka shiga Syria domin taimakawa ‘Yan tawaye, kamar adadin mayaka masu bin akidar Shi’a suka shiga kasar domin mara wa Gwamnatin Syria baya.

A shekarar 2013, akalla mayaka daga kasashen waje kimanin 600 ne aka ruwaito sun mutu wadanda suka shiga kasar Syria.

El Harun Muhammad na Babbar Kwalejin Fasaha ta Kaduna yace rikicin Syria ba ya da nasaba da banbancin akida idan aka yi la’akari da mayakan da ke yaki da Isra’ila.

A cewar El Harun akwai tsohuwar alakar kiyayya da manufofin kasashen yamma tsakanin Syria da Iran tun lokacin da aka yi juyin juya hali.

Samun yawaitar mayakan da ke shiga Syria babbar barazana ce ga zaman lafiya a duniya musamman a yankin Gabas ta tsakiya da Arewacin Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.