Ma'aikatan ma'adinan Africa ta Kudu sun shiga yajin aiki
Ma’aiakatan Ma’adanai a babbar cibiyar hakon Ma’adanin Platinum din kasar Afruka ta Kudu sun shiga yajin aiki, don nuna rashin amincwarsu da karin kudin harajin da ake karba a hannun su.Masu mallakar Filayen da ake hakar Ma’adanai da ke fuskantar tashin Harajin da kuma faduwar Riba, sun fada a fili cewar hakan ba zata sabu ba.Akalla Ma’aiakata Masu hakar Ma’adanai 80,000 ne da keda alaka da wata Kungiya mai kula da yanda ake hakar Ma’adanai a kasar suka shiga wannan yajin aikin, domin rashin amincewa da karin Harajin.Manyan kamfanonin sarrafa Ma’adanai wato Anglo-American Platinum da Inpala Platinum da kuma Lonmin duka sun tabbatar da yajin aikin.
Wallafawa ranar: