Isa ga babban shafi
Najeriya

Jam’iyyar adawa ta APC ta samu rijista a Najeriya

Hukumar zabe ta INEC a Tarayyar Najeriya ta amince da bai wa gungun jam’iyyun adawar kasar rejistar da ke ba su damar kasancewa jam’iyyar daya ta APC. Wannan kuma zai bai wa sabuwar jam’iyyar damar fafatawa da Jam’iyyar PDP mai mulki a zaben da za a gudanar a shekara ta 2015 a kasar.

Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega
Shugaban hukumar Zaben Najeriya attahiru Jega Bizwatch
Talla

Hukumar Zabe tace gungun Jam’iyyun adawa guda uku ACN da ANPP da CPC sun hade waje daya sun zama Jam’iyyar APC.

Hukumar zaben tace ta amince da matakin ne saboda jam’iyyun sun cim ma dukkanin bukatun da ake bukata na hadewa a waje guda.

An kwashe tsawon lokaci jam’iyyun suna kokarin hadewa domin kawo karshen mulkin Jam’iyyar PDP ta shugaba Goodluck Jonathan. Kodayake bai fito ya bayyana kudirin tsayawa takara ba amma ana sa ran PDP za ta sake ba Jonathan damar yin tazarce a zaben 2015.

An dade bangarorin Jam’iyyun adawar na samun baraka domin hadewa don kawo karshen PDP da ta kwashe shekaru sama da 10 tana shugabanci a Najeriya.

Batun tsayar da dan takara dai, shi ne babban kalubalen da kawance Jam’iyyun za su fuskanta saboda banbanci ra’ayin siyasa da bangaranci.

Jam’iyyar ACN ita ke da yawan Gwamnoni a yankin Kudu maso yammaci yayin da Jam’iyyar CPC ta Janar Muhammadu Buhari babban mai adawa da Goodluck Jonathan ke da kujerar gwamna guda a Nasarawa amma Jam’iyyar tana da tarin magoya baya a arewacin Najeriya.

Zaben 2015 a Najeriya kamar Mace mai ciki ce ba’a san me zata Haifa ba saboda kawancen Jam’iyyun na adawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.