Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta kudu na bukin cika shekaru biyu da samun ‘yancin kai

A yau kasar Sudan ta kudu ke bukin cika shekaru biyu da samun ‘yancin kanta daga Sudan, bukin da zai samu halartar akalla shugabannin kasashen Africa biyar.

Shugaban Sudan, ta KuduSalva kiir
Shugaban Sudan, ta KuduSalva kiir
Talla

A watan Janairun shekarar 2011 ‘yan kudancin Sudan, suka kada kuri’ar amincewa da ballewa, lamarin da ya sa ta zama ‘yar auta tsakanin kasashen duniya, bayan samun ‘yancin kai daga Sudan, kuma mamba ta 193, Majalisar Dinkin Duniya sa’annan ta 54 a kungiyar hadin kan Nahiyar Kasashen Afrika ta AU.

Bukin na yau na zuwa ne a daidai lokacin da ake ci gaba da samun takun saka tsakanin Sudan ta kudu da makwabciyarta, ta Arewa, lamarin da ke ci gaba da yin illa ga tattalin arzikin kasashen biyu.

Wasu daga cikin batutuwan da ke sa dangantaka tsakanin hukumin biranen Khartum da Juba na tsami sun hada da lamarin kan iyakar kasashen biyu, tsaro da man fetur din da ke kan iyakar ta su.

Masu lura da lamura na ganin har yanzu Sudan ta Kudu na kan matakan tsayawa da kafafunta, a daidai lokacin da take kokarin samun karin kawaye a ciki da wajen nahiyar ta Afrika.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.