Isa ga babban shafi
Mali

Dakarun Mali 63 tare da na yan tawaye 600 suka rasa rayukansu yanzu haka a yakin kasar

Rundunar Sojin kasar Mali, tace an kashe mata dakarun ta 63, yayin da aka kuma kashe Yan Tawaye 600 tun bayan kaddamar da yakin kasar a watan Janairu.

wasu dakarun sojan kasar mali a kauyen Kadji, le 1er mars 2013.
wasu dakarun sojan kasar mali a kauyen Kadji, le 1er mars 2013. REUTERS/Joe Penney
Talla

Kakakin sojin, Lt Col Souleyman Maiga, ya kuma ce an kashe sojojin kasashen Togo, Burkina Faso Fransa da Chadi, daga cikin sojojin da suka kai musu dauki.

A yayinda dakarun Kasar Britaniya 40 suka isa kasar Mali, dan horar da sojojin kasar, kan yadda zasu gudanar da aiyukan su, sakamakon matsalar Yan Tawayen da aka samu.

Rundunar sojin Britaniya tace, sojoji 21 sun isa Bamako, yayin da wasu 29 zasu same su can, kamar yadda kungiyar kasashen Tuari ta bukata.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.