Isa ga babban shafi
Libya

Hukumomin Libya na fuskantar barazanar zanga zanga shekaru biyu bayan mutuwar Ghaddafi

Kusan shekaru biyu bayan faduwar gwamnatin Tsohon Shugaban kasar Libya, hukumomi a kasar na fuskantar baranaza zanga zanga daga mutanen kasar a yayin da ake shirin wani gangamin tunawa da ranar da aka fara juyin juya halin da ya yi sanadiyar mutuwar Ghaddafi. A yanzu haka an girke jami’an tsaro a sassa daba daban na kasar na kasar a yayin da ake sa ran gudanar da zanga zangar a ran 15 ga watan Febrairu wanna shekarar.  

Wasu masu zanga zanga a kasar Libya
Wasu masu zanga zanga a kasar Libya
Talla

Masu shirya zanga zangar kamar yadda rahotanni ke nuna zasu bayyana bukantunsa wadanda suka hada da nuna rashin jin dadi ganin cewa kasar bata samu cigaba duk da juyin juya halin da aka yi, kana nuna rashin amincewa da saka wasu da suka rike mukamai a gwamnatin Ghaddafi a cikin gwamnati mai ci.

Wasu takardu da ake rabawa a kasar na dauke da sakon kira da a tunbike gwamnatin mai ci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.