Isa ga babban shafi
Kamaru

Babu matsalar cin zarafin Al’umma a Kamaru, inji Biya

Shugaban kasar Kamaru Paul Biya ya ce babu matsalar keta hakkin bil’adama a kasar Kamaru a lokacin da ya ke ganawa da shugaban Faransa Francois Hollande a birnin Paris. Shugaban ya yi watsi da zargin ana cin zarafin mutane a kasar shi.

Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yana ganawa da Shugaban Kamaru Paul Biya
Shugaban kasar Faransa Francois Hollande yana ganawa da Shugaban Kamaru Paul Biya REUTERS/Philippe Wojazer
Talla

A Watan Disemba ne kungiyar kare hakkin Bil’adama ta Amnesty international ta fitar da rahoto wanda ke zargin ana murkushe ‘Yan adawa da ‘Yan jaridu a kasar Kamaru.

Biya mai shekaru 79, tun a shekarar 1982 ne ya ke shugabanci a Kamaru.

Wani da ake zargin yana Luwadi Roger Jean-Claude Mbede yace an ci zarafin shi a kasar Kamaru tare da yanke ma sa hukuncin daurin shekaru uku a gidan yari.

A dokar kasar Kamaru ana yanke wa ‘Yan Luwadi hukuncin daurin shekaru Biyar idan an kama su amma Mbede an yanke masa hukuncin dauri shekaru uku akan zargin yana aikata luwadi.

Mista Mbede ya nemi afuwa daga Hollande na Faransa zuwa ga Shugaba Paul Biya domin janye hukuncin da a ka yanke ma shi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.