Isa ga babban shafi
Tunisia

Hukumomin Tunisia sun tsaurara matakan tsaro a kasar

Hukumomin kasar Tunisia sun karfafa matakan tsaro a wasu muhimman wurare da suka hada da zagayen ginin ofishin jakadancin kasar Faransa da ke birnin Tunis.

sojojin kasa da kasa a Mali
sojojin kasa da kasa a Mali AFP/ISSOUF SANOGO
Talla

Rahotanni sun ce tun kafin lokacin sallar juma’ar yau ne aka soma ganin jami’an tsaro a cikin damara suna zagayawa a muhimman wurare na birnin, inda kuma suka dora manyan shingaye a kan titunan da ke isa ofishin jakadancin na Faransa.

Tun a ranar larabar da ta gabata ne dai hukumomin Faransa suka bukaci dukkanin ‘yan kasar da ke zaune a Tunisia da su yi takatsantsan sakamakon abubuwan da ke faruwa a Algeria da kuma Mali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.