Isa ga babban shafi
Liberiya

Shugabar Liberiya ta gana da 'yan adawan kasar

Shugaban kasar Liberia Uwargida Ellen Johnson Sirleaf ta gana da bangaren ‘yan adawan kasar a wani abinda ake gani dabara ce domin kawo karshen sabanin dake kunno kai tsakanin ta, da ‘yan adawan.Wannan taro shine na farko da Shugaban kasar tayi da bangaren ‘yan adawan tun bayan zaben kasar data lashe, shekara yau daya kenan, a wa’adi na biyu na mulkin da take yi.Wata sanarwa daga Fadar Shugaban da ke Manrovia na cewa Shugaban ta tattauna da bangaren ‘yan adawa ne game da al’amuran da suka shafi kasa, da tsarin muki da kuma dokokin zabe a kasar. 

Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf.
Shugabar kasar Liberia, Ellen Johnson Sirleaf. REUTERS/Finbarr O'Reilly
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.