Isa ga babban shafi
Najeriya

Faruk Lawan yana hannun 'Yan Sandan Najeriya game da Badakalar Tallafin Mai

‘Yan Sandan Najeriya sun cafke Hon. Farouk Lawan shugaban kwamitin binciken badakalar Tallafin Mai. Wanda ake zargin ya karbi cin hancin kudi $620,000 daga hannun Femi Otedola.

Dan Majalisa Faruk Lawan
Dan Majalisa Faruk Lawan NAS
Talla

Rahotanni sun ce ‘Yan sanda sun ce ba zasu bada Farouk Lawan Beli ba kamar yadda lauyoyin shi suka bukata bayan kwashe lokaci mai tsawo ana tabka muhawara a daren jiya Alhamis.

A yau ne dai Majalisar Wakilan kasar za ta yi wani zama na musammman don duba batun zargin da ake wa Faruk Lawan na karbar toshiyar Baki karkashin jagorancin kwamitin da majalisar ta kafa, don binciken yadda ake gudanar da harakar tallafin man fetir a kasar.

Yanzu haka dai ‘Yan Sanda sun bukaci Faruk Lawan mika masu kudaden da ya karba na toshiyar baki ta hanyar Kwamishinan ‘Yan Sanda Ali Amadou.

Faruk Lawan yace ya karbi kudaden ne domin tona asirin kamfanin mai na Zenon Oil da yake samun matsin lamba daga Kamfanin.

Femi Otedola ne ya gabatar da wannan zargin yana mai cewa, Dan majalisar, Faruk Lawan ya karbi cin hanci ne domin fitar da kamfaninsa daga jerin kamfanonin da kwamitin majalisar wakilan ya bincika.

Wannan batun ne dai ya janye hankalin ‘Yan Najeriya inda suka zira ido domin ganin sakamakon badakalar daga kwamitin Faruk Lawan.

A farkon shekara ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya janye tallafin Man Fetir al’amarin da ya haifar da zanga-zanga daga sassan yankunan kasar.

A watan Fabrairun Katafaren Kamfanin hakar man Shell, ya ce Najeriya na hasarar ganga 150,000 na man kasar da ake hakowa kowacce rana, saboda yadda barayi ke sace man. Mataimakin shugaban kamfanin Shell mai kula da Nahiyar Afrika, Ian Craig, yace an samu raguwar masu fasa bututun mai, amma satar man na ci gaba da karuwa.

A cewar Mista Craig Najeriya na hasarar kashi bakwai cikin Dari a rana.

Najeriya ta dade tana fama da ‘Yan fashin bututun mai a yankin Niger Delta wanda ke haifar da hasarar miliyoyin gangar mai a rana. Amma Mista Craig Yace, bayan an yi nasarar shawo kan fasa bututun mai, yanzu wannan matsalar ce ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Mataimakin shugaban yace, bayan goyan bayan da barayin man ke samu a gida, suna kuma da masu taimaka musu daga kasashen waje, ta hanyar sayen man.

Kafin mutuwarsa, Tsohon shugaban Najeriya, Umaru Musa Yar’adua ya yi zargin manyan kasashen duniya da tallafawa barayin, wajen sayen abinda ya kira man da aka gurbata shi da jini.

Hukumar kula da makamashi a Najeriya, tace a halin yanzu kasar na hako gangar mai Miliyan biyu da dubu dari da tamanin kowacce rana, yayin da cin hanci da almundahana da rashin gaskiya ya dabaibaye aikin samar da man.

A Watan Janairu ne Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya rage farashin mai daga N141 zuwa N97, kusan kashi 30 domin kawo karshen zanga-zanga da yajin aikin da ma’aikata suka gudanar a cikin kasar.

‘Yan Najeriya dai suna ganin ta hanyar Tallafin Mai ne suke more arzikin da Allah ya Azurta kasarsu da shi.

Sai dai Najeriya ta dade tana fama da matsalar Cin Hanci da Rashawa, al’amarin da Masana su ke ganin shi ne tushen koma bayan ci gaban tattalin arzikin kasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.