Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridu

Sharhin Jaridun Afrika 18 ga Watan Afrilu 2012

Kotun Birtaniya zata bada umurnin kwace dukiyar Ibori na Najeriya. Yaki ya kusan barkewa tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu game da Man Fetir. Sojojin Guinea Bissau sun haramta gudanar da zanga-zangar kin jininsu.

Jaridu a Taswirar Africa
Jaridu a Taswirar Africa
Talla

Sudan da sudan ta kudu sun kama hanyar abka wa yaki da juna. Mai shiga tsakanin rikicin kasar na kungiyar Tarayyar Afrika Thabo Mbeki ya shaidawa kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya halin da kasashen biyu suka shiga tun bayan da Sudan ta kudu ta karbe ikon birnin Heglig mai arzikin mai.

Jaridar Sudan Tribune tace Sudan tana fuskantar matsin lamba bayan Asusun bada Lamuni na Duniya ya rage darajar tattalin arzikin kasar a shekarar 2012. Kuma yanzu farashin abinci a cikin kasar ya haura sama.

Jaridar Daily Nation a kasar Kenya tace kasar Kenya ta damu game da rikicin Sudan da Sudan ta kudu inda jaridar ta ruwaito Ministan yada labaran kasar Barnaba Marial Benjamin, yana kira ga bangarorin biyu su sansanta kansu.

A Najeriya Jaridar Punch, ta buga labari game da James Ibori tsohon Gwamnan Jahar Delta da kotun Birtaniya ta yanke wa hukuncin Daurin shekaru 13 a gidan yari.

Wani Wakilin Jaridar yace akwai yiyuwar Mista Ibori zai kwashe shekaru Biyar ne a gidan yari saboda ya kwashe shekaru Biyu a tsare kafin a yanke masa hukunci.

Jarida tace kotun Birtaniya zata bada umurnin karbe dukiyar Ibori don mayar da dukiyar ga Asusun Gwamnatin Jahar Delta.

Jaridar ta ruwaito cewa James Ibori ya mallaki gidaje biyu a birnin London da wani babban gida a birnin Johannasburg na kasar Afrika ta Kudu da wasu manyan Motoci masu tsada.

Jaridar Daily Nation a kasar Kenya ta ruwaito Labari game da Sojin kasar Guinea Bissau wadanda suka haramta gudanar da zanga-zangar kin jininsu bayan hambarar da gwamnatin farar hula kafin gudanar da zabe zagaye na biyu.

Jaridar tace haramci gudanar da zanga-zangar ya biyo bayan matakin da wasu matasa magoya bayan Gomes suka dauka domin gudanar da zanga-zangar la’antar Sojin kasar.

Tuni dai Kungiyar Tarayyar Afrika ta kakabawa kasar Guinea Bissau Takunkumi
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.