Isa ga babban shafi
Sharhin Jaridu

Sharhin wasu Jaridun Afrika

Tsagerun Neja Delta a Najeriya sun ce ‘Yan Boko Haram kada su yi gangancin taba Goodluck Jonathan. Jacob Zuma ya kara yin Aure a Afrika ta Kudu, kuma Matasan Jam’iyyar ANC sun ce Malema ne Shugabansu. Jaridun Uganda sun ruwaito lokacin da Museveni zai yi murabus. A kasar Kenya za’a haramta wa wasu ‘Yan siyasa tsayawa Takara.

Talla

Jaridar Star a kasar Afrika Ta Kudu ta buga babban labarinta game da sabon auren da shugaban kasar Jacob zuma ya yi karo na shida, kuma Jaridar tace Jacob Zuma ya tabbatar wa ‘Yan kasar gwamanatinsa ba zata kara yawan haraji ba bayan daura masa aure da matarsa ta hudu Bongi Ngema.

Sai dai Jaridar tace kudaden da ake kashewa a fadar Shugaban kasar zasu karu saboda sabon auren na Jacob Zuma.

Karkashin dokar kasar Afrika Ta Kudu akwai kudaden da ake ware wa Matan shugaban kasa. Amma a lokacin tsohon shugaba Thabo Mbeki ana ware kudaden ne ga matar shi daya Euro Miliyan uku a shekara amma yanzu kudaden sun linka saboda gwamnati tana kula da matan Jacob Zuma guda uku kafin ya sake yin wani Aure.

Jaridar tace Jam’iyyar Adawa ta DA ta lashi takobin gudanar da bincike game da yawan kudaden da ake kashe wa matan Shugaban kasa.

Sai dai labarin Jaridar Sowetan ya sabawa labarin Jaridar Star, domin Jaridar tace yawan Matan Zuma Biyar ne bayan ya auri Bongi Ngema. Kuma Jaridar ta karyata labarin da ke alakanta Gwamnati wajen kula da matan Shugaban kasa.

Jaridar Soweto ta sake ruwaito Labari game da Jam’iyyar ANC inda jaridar tace matasan Jam’iyyar sun ce Julius Malema ne suka sani a matsayin shugabansu.

A kasar Kenya Jaridar Daily Nation ta ruwaito labari game da dambarwar Siyasar kasar. A Cewar Jaridar gwamnatin kasar ta shirya wani zagon kasa ga ‘yan siyasa domin dakile kudirinsu na tsayawa takara.

Jaridar tace, hukumar zabe a kasar zata fito da wani tsari na haramtawa wasu tsayawa takarar zabe ta yin amfani da tantance cancantarsu da gaskiya.

Wasu daga cikin abubuwan da hukumar zata haramtawa ‘Yan Siyasa sun kunshi haramta gudanar da taro da dare da haramta kwarya kwaryan yakin neman zabe a fili ko a kafafen yada labarai.

Jaridar Daily Monitor ta kasar Uganda ta ruwaito labarin cewa a shekarar 2016 shugaban kasar Yoweri Museveni zai ajiye mukamin Shugaban kasa idan har Jam’iyyarsa ta bukace shi yin haka.

Museveni wanda ke shugabancin kasar Uganda tun a shekarar 1986, yana daya daga cikin shugabannin masu yawan shekaru a saman Mulki a Nahiyar Afrika.

A Wani Labarin kuma Jaridar Monitor a kasar ta Uganda, Ta ruwaito labari game da Najeriya, inda Jaridar tace kungiyar MEND da ke fafutikar ‘Yancin Neja Delta tace zata sa kafar wando guda da Kungiyar Boko Haram a Arewacin Najeriya idan suka aikata wani mummunan aiki ga shugaba Goodluck Jonathan.

Wannan kuma na zuwa ne bayan wani gargadi da Kungiyar Boko Haram ta yada a Intanet game da yunkurin karya gwamnatin Goodluck Jonathan.

Jariar ta ruwaito kalaman kakakin kungiyar Neja Delta Kaftin Mark Anthony yana cewa zasu kalubalanci Kungiyar Boko Haram.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.