Isa ga babban shafi
Libya

‘Yantawaye sun yi barazanar kifar da sabuwar gwamnatin Libya

Tsohon kwamandan ‘Yantawayen Libya ya yi gargadin dakarunsa zasu kifar da sabuwar gwamnatin Libya idan ta kasa cim ma bukatunsu na samun wakilci a sabuwar gwamnatin.A wata hira da kamfanin dillacin labaran Reuters, shugaban ‘Yantawayen Abdullah Naker yace sun sa wa gwamnatin ido kuma sun kusan yanke hukuncin matakin karshe.‘Yantawayen sun bukaci sabon Fira Ministan kasar Abdurrahaman El Kieb ya nada wasu daga cikin ‘Yantawayen cikin Ministocinsa in ba haka ba kuma su kaddamar da zanga-zangar lumana cikin kasar kamar yadda suka kifar da gwamnatin Ghaddafi.Kasa irin Libya da babu ‘Yan sanda ko Sojoji, samar da sabuwar gwamnati domin cim ma bukatar dubun dubatar ‘Yantawayen da ke dauke da muggan makamai abu ne mai wahala.A ranar Alhamis ne Naker ya gana da wakilan ‘Yantawayen a yankin gabacin Benghazi, inda suka bukaci lalle sai sabuwar gwamnatin kasar ta cim ma bukatunsu. 

Abdullah Naker Tsohon shugaban 'Yantawayen Libya lokacin da yake tattaunawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters
Abdullah Naker Tsohon shugaban 'Yantawayen Libya lokacin da yake tattaunawa da kamfanin Dillacin Labaran Reuters REUTERS/Ismail Zetouny
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.