Isa ga babban shafi
libya-ICC

Seif al-Islam yana kokarin tserewa daga Libya

Mai Gabatar da kara a kotun hukunta laifukan yaki, Luis Moreno Ocampo, yace Saif al-Islam, yana kokarin ficewa daga Libya ta hanyar taimakon wasu.A wani sako da ya aikwa kwamitin Sulhu na Majalisar Dunkin Duniya, Luis Moreno Ocampo ya yi kiran kasashen da ke makwabtaka da Libya toshe duk wata kafa ta shirin tserewarsa.Kotun tana kokarin sasantawa ne da Saif al Islam domin mika kansa bayan zarginsa da laifin aikata laifukan yaki.Mista Ocampo yace suna ci gaba da gudanar da binciken da ake zargin kungiyar NATO da dakarun ‘Yan tawaye wajen kashe fararen hula.Yanzu haka kuma Kotun ICC tace tana tattaunawa da masu shiga tsakani domin cim ma cafke Saif al-Islam bayan mutuwar mahaifinsa Kanal Gaddafi a ranar 20 ga watan Octoba.Wani rehoton da ba’a tabbatar ba shi ne cewa an ci karo da wata Tawaga dauke da Saif al-Islam da ta ratsa Sahara kan iyaka da Jamhuriyyar Nijar. 

Luis Moreno-Ocampo, mai gabatar da kara a kotun hukunta Manyan laifukan yaki ta ICC
Luis Moreno-Ocampo, mai gabatar da kara a kotun hukunta Manyan laifukan yaki ta ICC AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.