An zabi sabon Fira Minista a Libya
Gwamnatin wuccin gadi a kasar Libya, ta zabi Abdurahim al Kib, a matsayin wanda zai jagoranci Gwamnatin rikon kwarya, yayin da kungiyar kawancen tsaro ta NATO, ta kawo karshen yakinta a cikin kasar.Al Keib, wanda kwararen injiniya ne a fannin lantarki, ya fito ne daga Tripoli, kuma ya kada abokan takararsa hudu, da kuri’a 26 daga 51 da aka kada.Shugaban rikon kwarya, Mustafa Abdul Jalil, ya bayyana zaben shi a matsayin wani tabbaci cewar ‘Yan kasar Libya na iya gina makomarsu.Keib wanda malamin Jami’a ne kuma dan kasuwa, ya kwashe shekaru a kasashen waje wanda ya dade yana adawa da gwamnatin Muammar Gaddafi.Tun kafin zabensa kungiyar NATO ta bayyana kawo karshen yakinta a kasar Libya inda shugaban kungiyar Anders Fogh Rasmussen yace babu wata rawa da zasu taka bayan kawo karshen Gaddafi.
Wallafawa ranar: