Libya
An hango dan Gaddafi, Saif a kan iyakar kasar Niger
Fitaccen dan Marigayi Gaddafi, Seif al_islam wanda Kotun kasa-da-kasa tace tana neman shi, dazun nan wasu kafofi ke cewa an hango shi akan iyakan kasar Libya da Niger, yana neman tsallakawa zuwa Niger din.Wadanda sukayi tozali da shi suka ce bai shiga Niger din ba amma kuma yana gab da tsallakawa.Tun bayan da aka kashe mahaifin shi, hambararren shugaban kasar Libya Muammar Gaddafi, kungiyar tsaro ta NATO da gwamnatin wucin gadin kasar suka fara neman Saif, inda kuma ake fata in har an same shi, ya gurfana a gaban kotun ta kasa da kasa.
Wallafawa ranar: