Isa ga babban shafi
Najeriya

Mahara sun kashe dan jarida Nigeria

A Nigeria Wasu ‘yan bindiga, sun harbe wani dan jarida mai suna Zakariyya Isa da ke aiki da gidan talbijin din kasar wato NTA a daren jiya asabar. Wani da lamarin ya faru kan idon shi ya shaida wa kamfanin dillancin labarum kasar faransa AFP cewa, an harbi Zakariyya da misalin karfe 7 da rabi, a kofar gidan shi da ke unguwar Bulunkutu, yayin da ya fito daga masallaci.Mutumin mai suna Muhammad Musa yace da alama maharan sun biyo mutumin daga masallacin, suka kuma kashe yayin da ya zo dab da gidan shi.Wasu maharan daban kuma, sun far wa ofishin ‘yan sanda da bankuna 2 a garin Saminaka jihar Kaduna a daren na jiya, yayin da suka kasha mutane 3. 

Sufeto janar na 'yan sandan Nigeria Hafiz Ringin
Sufeto janar na 'yan sandan Nigeria Hafiz Ringin
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.