An kashe Mouammar Gaddafi na Libya
Wallafawa ranar:
Kunna - 20:00
A ranar Alhamis da ta wuce tashar Talibijin din Gwamnatin Rikon Kwarya na kasar Libya bayar da sanarwar hambararren Shugaban kasar Libya Moammar Gaddafi ya shiga hannunsu, a birnin Sirte. Abdel Majid, wani jamiin Gwamnatin Rikon Kwaryan ya fadi cewa an raunata Mommar Gaddafi a kafa.Sa’oi kadan bayan wannan sanawar, sai aka tabbatar da mutuwar Gadafi, lamarin da ya sa masu ruwa da tsaki suka yi ta bayyana ra’ayoyin su, wannan da sauran batutuwa, da suka hada da zanga zangar da aka yi a nahiyar Turai a karshen makon da ya wuce, da kuma musayar fursunnonin da kasar Isra’ila ta yi da Falasdinawa, sune za mu tattauna a cikin shirin na yau, wanda ni Nasiruddeen Muhammad zan gabatar, ayi saurare lafiya.