Isa ga babban shafi
Libya

'Yan tawayen Libya sun yi ikirarin Cafke Kanal Gaddafi

Wani kwamandan 'Yan Tawaye Mohamed Leith ya tabbatarwa kamfanin dillacin labaran Faransa AFP Cafke Kanal Gaddafi inda yace ya gan shi da idonsa jina-jina sanye da kakin Soji da rawani.Tun da safiyar yau  ne Gwamnatin ‘Yan tawayen  ta yi ikirarin karbe ikon birnin Sirte Mahaifar Kanal Gaddafi bayan kwashe tsawo sa’o’I biyu ana gudanar da yakin karshe a safiyar yau Alhamis. Birnin Sirte shi ne birni na karshe da ke karkashin ikon Gaddafi.An kwashe tsawon mako daya ana gwabza yaki a birnin Sirte duk da martanin da dakarun Gaddafi ke mayarwa a yankin Bani Walid da ke kudu maso gabacin birnin Tripoli.Tuni dai dai sabuwar Gwamnatin ‘yan Tawayen ta bayyana cewa karbe ikon birnin Sirte, shi zai bata damar tabbatar da nasararta akan Kanal Gaddafi kafin kafa sabuwar gwamnati.  

Wani dauke da tutar kasar Libya
Wani dauke da tutar kasar Libya RFI
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.