Isa ga babban shafi
Libya

Sarkozy Da Cameron suna ziyara a Libya

Shugaban kasar Faransa Nicolas Sarkozy da PM Birtaniya David Cameron sun wata ziyara zuwa kasar Libya yau Alhamis. Wannan ziyara ta zama ta farko, da shugabannin kasashen Duniya zasu kai kasar ta Libya, bayan tawayen da ya kawo faduwar gwamnatin Muammar Gaddafi ta shekaru 42. Kasashen na Birtaniya da Faransa ne suka wuce gaba wajen aiwatar da kudirin MDD, karkashin kungiyar tsaro ta NATO-OTAN, abunda ya baiwa ‘yan tawayen majalisar riko galba.Yayin ziyarar zuwa Tripoli babban birnin kasar ta Libya, Shugaba Sarkozy na Faransa da PM Cameron na Birtaniya, zasu gana da Shugaban riko na Libyan Mustafa Abdul Jalil, wanda ya yi alkawarin kafa tsarin demokaradiya bisa dokokin Islama mai sassaucin ra’ayi. Bernard-Henry Levy masani dan kasar Faransa daya tallafa wa tawayen yana cikin tawogar.Akwai kuma rohotanni dake cewa Shugaban zasu kuma ziyarci birnin Benghazi, inda tawayen ya samo asali. 

Nicolas Sarkozy da David Cameron
Nicolas Sarkozy da David Cameron Reuters/Benoit Tessier
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.