Isa ga babban shafi
Africa ta kudu

An yi daki ba dadi tsakanin 'Yan Sanda da Matasan jama'iyyar ANC a Africa ta Kudu

An kwantar da Wani dan sanda a asibiti, yayin da wasu ‘yan jaridu suka sami raunuka, yayin da aka dauki ba dadi tsakanin magoya bayan shugaban bangaren matasa na jama’iyyar ANC a Africa ta Kudu, Julius Malema, da ‘yan sandan kasar. Rikici ya barke ne yayin da magoya bayan Malema suka fara jifan ‘yan sanda da duwatsu da kwalabe, a kofar Shalkwatar Jama’iyyar ta ANC, yayin sauraren tuhumar da jama’iyyar ke wa Malema. Mai Magana da yawun ‘yan sandan birni Johanesbourg, Lungelo Dlamini yace wani katon dutse aka maka wa daya daga cikin ‘yan sanda da suka sami rauni, da kuma a halin yanzu yake asibiti, inda yace bai san halin da dan sandan ke ciki ba.Wata kafar yada labarum kasar tace a kalla ‘yan jarida 5 ne lamarin ya rutsa da su, yayin da aka jefe su da duwatsu.An kuma fasa gilasan motar. wani gidan talabijin din kasarJama’iyyar ANC mai mulkin kasar na tuhumar Malema da zubar mata da mutunci, da kuma nuna rarrabuwar kanu a tsakanin ‘ya ‘yanta, bayan da wasu rahotanni sun nuna cewa yana wani yunkuri na tumbuke Jacob Zuma daga shugabancin jama’iyyar. 

Reuters/Siphiwe Sibeko
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.