Isa ga babban shafi
afrika

Masu shan maganin HIV/AIDS za su iya rayuwa Mai tsawo

Wani rohoto ya nuna cewa, masu dauke da chutar kanjamau dake shan magani cikin kasashen Nahiyar Afrika, zasu iya tsawon rayuwa kamar sauran mutane. Masu bincike daga wata Jami’a ta Birtaniya, sun gudanar da nazari daga shekara ta 2000 zuwa 2009 da mutane 22,315 ‘yan kasar Uganda.An kwantanta rayuwar masu dauke da cutar ta kanjamau da shekaru 55, da akalla mutane ke rayuwa kafin mutuwa a kasar Uganda, kuma aka gano zasu iya kusan wannan rayuwar idan suna shan magani.Binciken ya gano cewa ‘yan shekaru 35 da suka kamu da chutar zasu sake rayuwa ta akalla karin shekaru 22 maza ke nan, amma mata zasu iya kara shekaru 32 a raye.Haka na da nasaba da yadda maza ke lattin zuwa wajen karbar magani, ba kamar mata ba.Wannan ya zama bincike mafi girma game da tsawon rayuwar masu dauke da chutar ta kanjamau cikin kasashen Kudu da Sahara na Afrika.Chutar ta hallaka kimanin mutane milyan 30, cikin shekaru 30, daga shekarar 1981. Yayin da wasu milyan 34 ke dauke da ita. 

Ma'ajiyar Magungunan HIV/AIDS
Ma'ajiyar Magungunan HIV/AIDS
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.