Isa ga babban shafi
Libya

NATO ta fadada hare hare kan Libya

Sa’o’i biyu da ta kaddamar da hare hare a Tripoli, jekadun kungiyar Kawancen ta NATO ko OTAN suka amince da yarjeniyar ci gaba da yaki a Libya har zuwa watan Satumba lokacin da suke ganawa a Brussels.A cewar shuagaban rundunar ta NATO, Anders Fog-ras masin, sun yanke wannan hukuncin ne domin ci gaba da kare fararen hula a Libya tare da kare manufofin majalisar Dunkin DuniyaA 27 ga wannan watan ne dai yarjejeninayar NATO zata kawo karshe a kasar Libya, sai dai kuma kungiyar tace kara wa’adin watannin biyu zai basu damar kara shirin karya shugaba Gaddafi.A daya bangaren kuma gwamnatin Libya tace hare haren da Nato ke kaiwa ta jiragen sama yayi hasarar mutuwar fara faren hula sama da 700 tare dajikkata mutane sama da 4000.Sai gab da yanke wannan hukuncin na kungiyar NATO, Kungiyar tarayyar Africa ke bayyana nuna goyon bayanta ga kasar Rasha na shiga tsakanin rikicin. 

Reuters/Louafi Larbi
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.