Isa ga babban shafi
Libya

An kai wa hukumomin Isra’ila sakon ‘yan tawayen Libya

Wani marubuci dan asalin kasar Faransa, Benard henry Levy, yace ya isar da sakon ‘yan tawayen kasar Libya ga hukumomin Isara’ila, inda ‘yan tawayen suka bayyana cewa za su nemi kulla huldar diplomasiyya da Isra’ila in suka kafa Gwamnati. Levy, wanda ya taimaka wajen amincewar da hukumomin Faransa da suka yi wa ‘yan tawayen, ya kai ziyara birnin Bengazi da ke hannun ‘yan tawayen na Libya.Ya kuma ce hukumomin kasar Isra’ila sun yi na’am da sakon da ya kai musu. 

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.