Isa ga babban shafi
Nijar

Kotu ta wanke tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja daga zargin handamar kudin jama’a.

Kotun daukaka kara ta birnin Yamai,ta yi watsi da dukan zarge-zargen da ake ma tsohon shugaban kasar Mamadou Tandja,kamar yadda lauya Souley Oumarou daya daga cikin lauyoyin da ke kare tsohon shugaban kasar ya sanar.Ya furuta cewa a yau shugaban kasar na baro gidan kason garin Kollo in da ake tsare da shi tun cikin wata Janeru. An dai tuhumi tsohon shugaban kasar ne da handame kudin kasa mliyar 4 na kudin sefa kimanin Yiro milyon 6.Haka kuma ana zargin shi da rufe ido kan hukumcin kotn tsarin mulkin kasar domin ci gaba da zama kan kujerar mulki . 

Tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja
Tsohon shugaban kasar Nijar Mamadou Tandja AFP
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.